Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban kasar Najeriya ya zargi kasashe masu arziki da jibge makamai a Afrika


Nigerian President Goodluck Jonathan (File)

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya zargi kasashe masu arziki da jibge makamai a kasashen nahiyar Afrika inda suka karasawa a hannuwan masu aikata miyagun laifuka da kuma mayaka.

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya zargi kasashe masu arziki da jibge makamai a kasashen nahiyar Afrika inda suka karasawa a hannuwan masu aikata miyagun laifuka da kuma mayaka. Da yake jawabi a wajen wani taron kiyaye zaman lafiya a birnin tarayya Abuja jiya litinin, Mr. Jonathan yace shigar da makamai kasashen nahiyar Afrika da kasashe masu arzikin masana’antu ke yi, yana daga cikin manyan matsaloli dake addabar nahiyar. Shugaban kasar Najeriyan ya kuma yi barazanar janye dakarun Najeriya dake aikin kiyaye zaman lafiya karshin shirin MDD, muddar ba a sauya sharudan ayyukan kiyaye zaman lafiya ba. Sai dai bai bayyana irin canje canjen da yake bukatar gani an yi ba.

Nigerian militants.
Nigerian militants.

Ya dai bayyana cewa ba za a lamunci kashe wani sojan najeriya yayinda yake aikin kiyaye zaman lafiya sakamakon kwantan bauna da kungiyoyin mayaka ke yi ba. Kawo yanzu Najeriya tana da sojoji dubu shida dake aiki karkashin shirin kiyaye zaman lafiya na MDD a kasashe daban dabam na duniya.

XS
SM
MD
LG