Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadansu ‘yan bindiga sun kai hari a gidan tsohon mataimakin gwamnan jihar Bayelsa


Rundunar ‘yan sandan Najeriya tace wadansu mahara da ba a san ko su wanene ba sun kai harin bom a gidan wani fitaccen dan siyasa a yankin Niger Delta mai arzikin man fetir ta kasar.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya tace wadansu mahara da ba a san ko su wanene ba sun kai harin bom a gidan wani fitaccen dan siyasa a yankin Niger Delta mai arzikin man fetir ta kasar. Rundunar ‘yan sanda ta bada tabbaci yau asabar cewa, maharan da suke cikin wadansu kananan jiragen kwale-kwale masu gudu sun jefa nakiyoyi a gidan tsohon mataimakin gwamnan jihar Bayelsa Peremobowei Ebebi. Ebibi ya shafe makonni a babban birnin tarayya Abuja. Sai dai shaidu sun ce an harbi wani mai gadi aka ji mashi rauni yayin harin. Wadansu rahotanni sun nuna cewa an kashe mai gadin. Ebibi ya jima yana rikicin siyasa da gwamna Timipre Sylva. Watan jiya ‘yan majalisar dokokin jihar suka tsige shi daga mukaminsa.Rundunar ‘yan sandan Najeriya tace wadansu mahara da ba a san ko su wanene ba sun kai harin bom a gidan wani fitaccen dan siyasa a yankin Niger Delta mai arzikin man fetir ta kasar. Rundunar ‘yan sanda ta bada tabbaci yau asabar cewa, maharan da suke cikin wadansu kananan jiragen kwale-kwale masu gudu sun jefa nakiyoyi a gidan tsohon mataimakin gwamnan jihar Bayelsa Peremobowei Ebebi. Ebibi ya shafe makonni a babban birnin tarayya Abuja. Sai dai shaidu sun ce an harbi wani mai gadi aka ji mashi rauni yayin harin. Wadansu rahotanni sun nuna cewa an kashe mai gadin. Ebibi ya jima yana rikicin siyasa da gwamna Timipre Sylva. Watan jiya ‘yan majalisar dokokin jihar suka tsige shi daga mukaminsa.

XS
SM
MD
LG