Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon shugaban Nijer Tandja Mamadou, ya aika da takardar neman gafara ga gwamnatin mulkin sojin kasar


Shugaban gwamnatin mulkin sojan Junhuriyar Nijer, Manjo Salou Djibo, wanda ya kwace ragamar mulki ran 18 ga watan Fabrairun 2010 daga hannun tsohon shugaba Tandja Mamadou. (file photo)

Tsohon shugaban Nijer Tandja Mamadou, ya aika da takardar neman gafara ga gwamnatin mulkin sojin da ta hambaras da shi.

Tsohon shugaban Nijer Tandja Mamadou, ya aika da takardar neman gafara ga gwamnatin mulkin sojin da ta hambaras da shi. Tandja Mamadou, mai shekaru 72 da haihuwa a wasikar da ya tura yana cewa bashi da koshin lafiya, kuma ba zai iya fuskantar kotun soja ba, yace ya gwammace ayi masa tsarewar talala a gidansa maimakon fuskantar kotun soja.

Tandja Mamadou (file photo)
Tandja Mamadou (file photo)

A watan Fabarairu ne soja suka hambaras da Gwamnatin Tandja Mamadou, sannan soja suka kafa hukumar yaki da cin hanci da rashawa wadda zata binciki duk zargin da ake yiwa jami’an Gwamnatin Tandja na yin sama da fadi da dukiyar jama’a.

XS
SM
MD
LG