Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Addinai Sun Alakanta Ayyukan Ta’addanci Da Tsatsauran Ra’ayi


Taron zaman lafiya a Kaduna 1.

Ganin yadda ake yawan samun ta'addanci da kai hare-haren da aka hallaka mutane a wasu yankunan Najeriya, ya sa cibiyar wanzar da zaman lafiya da ke Kaduna, ta tara malaman addinin musulunci da shugabannin kiristoci domin fahimtar juna da kuma kawar da yaduwar tsatsauran ra'ayi.

Taron kwanaki ukun da ya tattauna hanyoyin nemo maslaha game da abubuwan dake kawo rikice-rikice da kuma hare-hare ya cimma matsayar yada fahimtar juna tsakanin mabiya addinai a Najeriya.

Pastor James Mobel Wuyeh shine jagoran cibiyar da ta shirya wannan taro kuma ya an gayyato malaman makarantun Islamiya da masu koyarwa a coci coci da kuma manya manyan malamai masu jama’a.

Yace dalilin shirya wannan taro shine domin a takawa masu tsatsauran ra’ayi na addini, su san yadda zasu dinga sarrafa maganganu musamman su daina shige iyaka. Kuma domin a dawo da hankalin wadanda tunaninsu yayi zurfi ta wannan fannin.

Ya kuma kara da cewa su kara jan hankalin malamai su koyar da darrusa da zasu hana mutane shiga halin wuce gona da iri a addini.

Mahalarta taron kwanaki ukun da aka yi a Kaduna sun ce irin wannan taro na iya dinke barakar da ke tsakanin mabiya addinai.

Babban burin wannan taro dai shine nuna wa malaman addinai muhimmancin da ke da akwai wajen ganin sun janyo mabiya don ganin basu shiga ta’addanci ko tada hankulan al’umma ba.

Dama dai wasu masana harkokin tsaro na ganin dole al-umma su rinka shinfida shirin fahimtar juna don magance matsalolin tsaro maimakon zubawa gwamnati ido duk lokacin da rigima ko rikici ya taso.

Saurari cikakken rahoton Isa Lawal Ikara:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00


Facebook Forum

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG