Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afrika Na Taro a India


Taron shugabannin kasashen Afrika

Yau Litinin aka bude wani taro da kasar India ta shirya da kafatanin kasashen Afrika, inda za a kwashe kwanaki hudu ana tattaunawa kan batutuwan da suka shafi kasashen da kasar ta India a birnin New Delhi.

Batun da ya mamaye wannan taro kamar yadda rahotanni suka nuna shi ne batun kasuwanci da yadda kasar ta India za ta kara kusantar nahiyar ta Afrika.

Da yawa daga cikin masu fashin baki kan harkokin kasashen waje, suna kallon wannan taro a matsayin wani yunkuri da India ke yi na gasa da kasar China wacce wasu ke ganin ta yi kane-kane a nahiyar.

Taron yana gudana ne a karkashin Firai ministan India, Narendra Modi, wanda ya gayyaci dukkanin kasashen Nahiyar su 54.

Shi ne kuma na uku cikin ire-iren taruka da India ta shirya a baya da ya shafi kasashen Afrika, inda a shekarar 2008 aka yi a New Delhi da kuma 2011 da aka yi Addis Ababa.

Kasashen na nahiyar Afrika na samun wakilcin shugabanninsu ko kuma wasu manyan jami’an gwamnatinsu.

A gobe Talata ake sa ran shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, zai halarci taron, kamar yadda wata sanarwa da mai bashi shawara na musamman kan harkar ‘yan jarida, Femi Adesina ya fada.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG