Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afirka Ta Kudu: Zanga Zangar Daliban Jami'a


Students burn portable toilets during their protest against university tuition hikes outside the union building in Pretoria, South Africa, October 23, 2015.

'Yan Sanda a Afrika ta Kudu sun yi amfani da gurnetin roba wajen tarwatsa dalibai da suka yi zanga zanga yau Jumma’a a harabar fadar gwamnatin kasar.

Dubban dalibai sun taru a harabar ofishin dake Pretoria domin nuna adawa da shirin gwamnati na kara kudin makaranta. Ofishin Shugaba Jacob Zuma yace yana wata ganawa ta dabam da shugabannin zanga zangar da kuma ofishin harkokin ilimi a yunkurin shawo kan rikicin.

Shaidu sun ce wadansu masu zanga zanga kalilan sun rika jifar ‘yan sanda a harabar ofisoshin. Wadansu kuma suka ciccina wuta da ‘yan sanda suka kashe da mesar ruwa.

Zanga zangar da dalibai suka shafe makonni suna yi, ta nuna adawa da karin kashi goma bisa dari na kudin makaranta, ya tilasta jami’oi goma sha hudu rufewa na dan lokaci.

XS
SM
MD
LG