Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashen Duniya Sun Fara Mahawara A Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya


Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya
Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya

Dukkan shugabannin suna fara jawaban su ne da batun annobar coronavirus da ta hana gudanar da taron na gaba da gaba a bara da kuma yanda annobar ta kawo nakasu ga shirin muradun karni da ma tattalin arzikin duniya.

Sama da shugabannin kasashe 30 ne suka gabatar da jawabansu, wasu a zauren taron wasu kuma ta hoton bidiyo daga kasashensu. Kimanin kasashen Afrika hudu ne suka gabatar da jawabansu da suka hada da Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo da Misra da Somalia da kuma Zambia.

Shugaban Amurka Joe Biden da ya yi jawabi na biyu a zauren taron bayan da shugaban kasar Brazil, Jair Bolsonaro ya kammala nasa jawabin, wannan ne karon farko da ya halarci taron kolin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a matsayin shugaban kasa kana ya fara jawabinsa ne da bayyana wa duniya cewa Amurka za ta ci gaba da aiki tare da sauran kasashen duniya.

Biden ya kare shawarar janye sojojin Amurka daga kasar Afghanistan, sai dai kuma ya bayyana irin gudunmuwar da Amurka ke bayarwa a yaki da annobar COVID-19, yana mai cewa tuni Amurka ta saka dala biliyan 15 a yaki da COVID-19 a duniya.

Ya ce mun aike da sama da allurar rigakafi miliyan 160 zuwa ga wasu kasashe, ciki da har allura miliyan 130 da mu kan mu muka raba da kuma kashin farko na allurar rigakafi rabin biliyan guda da muka saya daga Pfizer muka bai wa shirin tallafin rikagaki na COVAX.

Shi ko sabon shugaban Iran Ebrahim Raisi ya fara jawabin sa ne da caccakar takunkuman da Amurka ta dora wa kasarsa a matsayin wani yaki a kaikaice kana ya yi amfani da jawabinsa na farko a Majalisar Dinkin Duniya a matsayin shugaban kasa ya yi kira ga Washington da ta sake duba manufofinta a yankin da kuma siyasar rarraba kawuna a Amurka.

“Yanzu takunkumai ne wata sabuwar dabarar da Amurka ke amfani da ita tana yaki da kasashe,” inji Raisi, ya kara da cewa wannan jan kunne a lokacin annobar COVID-19 ya kai a kira shi da laifin cin zarafin bil Adama.

Shugaban China Xi Jinping, yana cikin shugabannin manyan kasashe da suka yi jawabi a ranar farko na taron kolin Majalisar Dinkin Duniya wanda shi ma ya ce dimokaradiya ba hakki ne na wata kasa daya ba, illa tsari ne da mutanen kowace kasa zasu mora.

Shugaba Xi, ya yi alkawarin cewa China zata ci gaba da kokarinta na yin aiki tare da MDD zuwa ga wani matsayi kana zata bada muhimman taimako ga kyawawan ayyuka da Majalisar ke yi.

Shugaban kasar Somalia Mohamed Abdullahi Mohamed da ya gabatar da jawabinsa ta hoton bidiyo ya ce Covid-19 ta yi mummunan tasiri a kan tattalin arzikin Somalia kamar kowace kasa a duniya, amma wannan bai sa kasar ta karaya ba wurin kokarin farfado da tattling arzikinta, ya ce “nasarar da muke samu wurin wadannan sauye sauye ta karfafa yarda tsakanin gwamnatin Somalia da jama'a da ma abokan huldarmu na kasa da kasa.”

Mohammed Mada jami’i ne a ofishin Magajin Garin birnin New York wanda yake bibiyan taron. Ya bayyana irin sakon da da yake so ya ga sauran kasashen Afrika da zasu yi jawaban a wannan taron su bayar. Ya ce ya kamata su maida hankali wurin allurar rigakafi ta yanda zasu taimako daga masu hannu da shuni saboda galibin kasashen Afrika basu da kudin sayan rigakafin.

Mada ya kuma tabo batun kasuwanci, inda ya ce akwai bukatar kasashen Afrika su nemi tallafin kasuwanci saboda irin barnar da annobar COVID-19 ta yi wa harkokin kasuwanci da tattalin arziki a kasashen Afurka.

Ana nan ana ci gaba da tafka mahawara a zauren taron na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.

Baba Yakubu Makeri daga birnin New York:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:01 0:00


XS
SM
MD
LG