Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashen Duniya Sun Taya Biden Murna


Kasar koriya ta kudu ta taya Joe Biden na jam’iyyar Democrat murna bisa nasarar da ya samu kan Shugaba Donald Trump a zaben shugaban kasar Amurka mai zafi da aka yi.

Shugaban na koriya ta kudu Moon Jae-in ya rubuta wani dan takaitaccen sako ta shafin sada zumuntarsa ranar Lahadi 8 ga watan Nuwamba ya na bayyana goyon bayan sa ga tsohon mataimakin Shugaban na Amurka da mataimakiyarsa Sanata Kamala Harris.

Haka kuma shugabannin kasashen duniya ciki har da Firai Minista Boris Johnson da Shugabar Jamus Angela Merkel sun taya Joe Biden Murna a jiya Asabar bayan da sakamakon kuru’u daga jihar Pennyslvania ya yi hasashen Biden ne ya lashe zaben.

“Amurka muhimmiyar kasar huldarmu ce kuma ina fatan zamu yi aiki tare akan abubuwan da muke ba fifiko, kama daga batun sauyin yanayi zuwa harkokin kasuwanci da kuma tsaro,” a cewar Johnson a wata sanarwa da fadarsa ta fidda.

Wasu magoya bayan Trump sun bayyana bakin cikinsu akan shugabannin kasashen na ketare.

Cikin shugabannin kasashen duniya na farko-farko da suka maida martini akan hasashen cewa Biden ne ya lashe zaben shine Firai Ministan Canada Justin Trudeau.

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Hira da Yusuf, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da ya shekara a Abuja yana sana’r gyaran takalmi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
XS
SM
MD
LG