Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashen Eritrea da Habasha Sun Yi Ganawar Tarihi


Firai Ministan Ethiopia Abiy Ahmed, da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki
Firai Ministan Ethiopia Abiy Ahmed, da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki

Shugabannin kasashen Eritrea da Ehiopia sun rungumi juna a tashar kasa da kasa ta Asmara yau lahadi, wani abin tarihi a daya daga rikicin da aka jima ana tafkawa a nahiyar Afrika.

Ganawar tsakanin shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki da Firai Ministan kasar habasha Abiy ahmed ta share fagen dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Taron kolin da ake gudanarwa a babban birnin kasar Eritrea Asmara, shine na farko da shugabannin gwamnatocin suka gudanar tun shekara ta dubu biyu, lokacinda Afwerki, da tsohon PM kasar Habasha Meles Zenawi ya sa hannu a yarjejeniyar da ake kira yarjejeniyar Algiers, da ta kawo karshen rikici tsakanin kasashen biyu da ya janyo asarar rayuka.

Kasar Habasha taki aiwatar da yarjejeniyar da ta bukaceta ta shata kan iyakar kasashen biyu, bayan shekaru biyu da sa hannu a yarjejeniyar ta Algiers, Habasha ta ci gaba da mamaye filin dake kusa da kotun kasa da kasa da aka ba Eritrea.

Wannan ya janyo yakin cacar baki tsakanin kasashen biyu na kusan shekaru ishirin, da yafi shafar kasar Eritrea da bata da girma.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG