Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Rasha da Faransa Sun Cimma Matsaya Akan Yaki da ISIS


Shugaba Vladmir Putin

Shugaban Faransa Francois Holande, yace shi da shugaban Rasha Vladimir Putin, sun yarda zasu yi musayar bayanan sirri dangane da mayakan sakan kungiyar ISIS da wasu kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi domin tabbatar nasarar farmakin da suke kaiwa da jiragen yaki.

"zamu yi musayar bayanai dangane da wadanda zasu kai wa hari da wadanda zamu kyale," inji shugaba Hollande a wani taro da manema labarai bayan da shugabannin biyu suka gana a birnin Moscow. "Abunda muka yarda shine, kuma wannan yana da muhimmanci, shine zamu kaiwa Daesh hari, amma zamu kaucewa dakaru da suke yakar ta'addanci."

Shugaba Putin yace a shirye kasarsa take domin ta hada kai tsakaninta da Faransa da kuma Amurka wajen zaben muradun ISIS da zasu kaiwa hari.

Shugaba Hollande yaje Moscow ne domin neman a hada karfi da karfe kan kungiyar ISIS mataki da ya kawo shi nan Amurka, ya kuma kaishi Jamus, da Britaniya da kuma kasar Italiya.

XS
SM
MD
LG