Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Soja Ya Harbe Soja Ya Kashe Kansa a Korea Ta Kudu


Kafafun Wasu Sojojji

A halin da ake ciki, wani sojan kasar Korea ta Kudu na wucin gadi ya harbe wani takwaransa aikinsa ya kuma raunana wasu uku kafin ya harbe kan sa.

Yau laraba, jami’an kasar Korea ta kudu suka ba da rahoton cewa mutumin ya fara harbin fada kan mai uwa da wabi a lokacin da suke rawar daji a birnin Seoul.

Dokar kasar ta tanadi cewa ‘yan tsakanin shekara goma sha takwas zuwa talatin da aka tsara da nufin tinkarar barzanar tsaro daga makwabciyar ta Korea ta arewa.

Bayan sun kammala aikin sojan na tilas, an kuma tanadi cewa tilasa kuma mutum ya yi wasu shekaru a zaman sojan wucin gadi, ana iya masa horo akai-akai.

Rahotanni sun bayyana cewa yin harbi tsakanin sojojin Korea ta abu ne da aka saba gani, to amma ba kasafai ake ganin haka tsakanin sojojin wucin gadi ba.

XS
SM
MD
LG