Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Armenia Sun Kai Hari Garin Ganja


Harin garin Ganja
Harin garin Ganja

Fadan da ake yi tsakanin sojojin Armenia da Azerbaijan kan yankin Nagorno-Karabakh ya bazu har zuwa bakin iyakokin yankin da ake takaddama a kansa jiya Lahadi 4 ga watan Oktoba. 

Hikmet Hajiyev, wani hadimin shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev, ya ce sojojin Armenia sun yi barin wuta da manyan bindigogi da rokoki a garin Ganja wanda shi ne gari na biyu mafi girma a Azerbaijan, inda suka kashe akalla mutum daya tare da raunata wasu talatin da biyu.

Hajiyev ya kara da cewa sojojin na Armenia sun kuma kai hari a Mingachevir, birnin da ake hada-hadar kasuwanci sosai da kuma wasu kananan garuruwa.

Jami’an tsaron Armenia sun musanta ikirarin Hajiyev, amma Arayik Harutyunyan, shugaban yankin Nagorno-Karabakh da ake takaddama akansa, ya fada a wani sako da ya wallafa a shafin Facebook cewa dakarunsa sun auna wuraren sojoji a Ganja kafin ya umurce su da su daina don kaucewa kisan farar hula.

Harutyunyan ya yi gargadin cewa dakarunsa zasu fara kai hari kan sauran manyan biranen Azerbaijani kuma ya bukaci mazauna biranen su tashi ba tare da bata lokaci ba

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG