Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Saman Najeriya Sun Kashe 'Yan Boko Haram A Jihar Borno


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

A wani babban cigaba a yaki da ta'addanci, rundunar mayakan saman Najeriya ta ce sojointa sun hallaka wasu mayakan Boko Haram.

Hedkwatar rundunar sojojin saman Najeriya ta ce jiragen yakinta sun kai wani kazamin hari a wani sansanin mayakan Boko Haram a arewacin jihar Borno.

Kakakin rundunar Air commander Ibikunle Daramola ya shaidawa muryar Amurka cewa tunda farko bayannan sirri sun nuna cewa yan Boko Haram din na amfani da wurin a matsayin wurin horaswa, sannnan an Kuma gano wasu tarin mayakan a wurin, inda nan take Kuma jiragen yaki samfurin Alpha jet suka masu dirar mikiya sukai masu kaca kaca.

Air commander Daramola, kazalika ya ce mayakan saman sunkuma gani wani jerin gwanon motocin mayakan na Boko Haram Dauke da miyagun Makamai inda suma aka masu rugu rugu a wajajen yankin Tumbin Rego.

Masanin Tsaro Wing commander musa isa salman ya ce ire iren wannan hari na nuna cewa ka iya tabbatarwa Boko Haram cewa babu inda zasu buys, duk inda suka shiga jiragen sojin sama ka iya zakulosu Kuma ai maganinsu.

Shima Mai Sharhi kan sha'anin Tsaro Mallam Kabiru Adamu yace yan da kyau mutanen dake shiyyar Arewa maso gabas Suke bada goyon baya ga dakarun ta hanyar sanar masu da bayannan sirri.

A cewarsa. Sha'anin Tsaro alhakine da ya rataya a wuyan Kowa da Kowa wajen samun Nasara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG