Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Syria Sun Hallaka Mutane Fiye da Dari A Yankin 'Yan Tawaye


Mayakan da suke da goyon bayan Turkiya suna rike da makamansu
Mayakan da suke da goyon bayan Turkiya suna rike da makamansu

Jiya Talata sojojin gwamnatin Syria suka hallaka mutane fiye da dari a yankin dake hannun 'yan tawaye a kokarin cafke wurin da yake da kurdawa da dama lamarin da ya sa Turkiya ma na kokarin kutsawa da sojojinta

Wata cibiyar dake sanya ido a kan rikicin da ake yi a kasar Syria ta ce farmaki da sojojin gwamnati suka kai a jiya Talata a wata gunduma mai suna Ghouta dake hannun 'yan tawayen a bangaren gabashin Damascus, ya kashe sama da mutane dari.


Wata kungiyar rajin kare hakkin dan adama ta kasar Syria dake Birtaniya, tace akalla mutane 250 ne aka kashe tun daga yammacin ranar Lahadi, hari mafi muni tsakain sa’o’I 48 da aka kai a cikin yakin Syria, tun bayan harin guba da aka kaiwa gundumar a shekarar 2013


A jiya Talata, sojojin Turkiya sun tilastawa sojojin gwamnatin Syria suka koma baya, a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa yankin Afrin na kasar Syria, yankin da sojojin kasar ta Turkiyya take gwabza fada da dakarun Kurdawa har na tsawon wata guda.


Gidan talbijin na Syria ya nuno ayarin rokoki kimanin ashirin suna shiga yankin Afrin daga kauyen Nubul.


Aikewa da sojoji na zuwa ne wuni guda bayan da Turkiya ta yiwa gwamnatin Syria kashedi, kada ta shiga yankin, cewa zata mai da martani idan sojojin Syria suka yi kokarin kare mayakan Kurdawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG