Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Soludo Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Anambara


Charles Chukwuma Soludo, Zababben gwamnan jihar Anambara

Soludo yayi takara ne a karkashin inuwar jam’iyyar APGA mai mulkin jihar, inda ya kayar da abokan takararsa 18, manya daga cikinsu, Valantine Ozigbo na jam’iyyar PDP, da kuma Andy Uba na jam’iyyar APC.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Charles Chukwuma Soludo, ya lashe zaben gwamnan jihar Anambara da ke kudu maso gabashin kasar.

Jami’ar tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Anambra, Farfesa Florence Obi ce ta ba da sanarwar sakamakon zaben bayan kammala tattara shi da sanyin safiyar Laraba.

Soludo yayi takara ne a karkashin inuwar jam’iyyar APGA mai mulkin jihar, inda ya sami kuri’u dubu 112 da 229, inda kuma ya kayar da abokan takararsa 18, manya daga cikinsu, Valantine Ozigbo na jam’iyyar PDP da ya sami kuri’u dubu 53 da 807, da kuma Andy Uba na jam’iyyar APC, wanda ya sami kuri’u dubu 43 da 285.

Tun a daren Lahadi aka sami tattara sakamakon zaben kananan hukumomin mulki 20 daga cikin 21 na jihar, to sai dai kuma babbar jami’ar tattara sakamakon zaben ta bayyana cewa zaben bai kammala ba, har sai da aka sake gudanar da zabe a karamar hukumar Ihiala a ranar Talata.

XS
SM
MD
LG