Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somalia Na Shirin Zaben Shugaban Kasa Da Na 'Yan Majalisa Cikin Zaman Tankiya


Shugaban Somalia Mohamed Abdullahi

Yayin da Somalia ke cika shekaru 30 da rushewar mulkin kama karya a kasar da kma rikice rikice da suka addabi kasar, gwamnatin ta shirya gudanar da zaben kasa mai cike da rikici.

Wasu jihohin kasar biyu sun ki shiga zaben na shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin Somalia, yayin da lokacin da aka kayyade na ranar takwas ga watan Janairu ke karatowa.

Dokar majalisa ta baiwa shugaban kasa Mohamed Abdullahi Mohamed da ‘yan majalisar dokoki su ci gaba da aiki, amma idan suka haura ranar takwas ga Faburairu, akwai yiwuwar fadawa cikin wani mummunar rikicin siyasa a kasar da ba a bukatar irin wannan tarzoma, inji wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman James Swan, ya fada a wannan mako.

A cikin kafa allunar gangamin neman zabe da yin jawabai a babban birnin kasar, Mogadishu akwai alamun damuwa a birnin, yayin da ake kira ga mutane su marawa ‘yan takaran baya amma kuma ba zasu iya yin hakan kai tsaye ba.

Zaman tankiya da ake yi a kasar ka iya baiwa kungiyar ta’addancin Somalia ta al-Shabab damar kai hare hare, wacce a baya ta yi barazanar kai hari a runfunar zabe.. A hali da ake ciki, yanzu ne kuma kasar take kokarin cike gurbin sojojin Amurka 700 da aka janye su, wani aiki da aka kammala a cikin watan Janairu.

Samun nasarar gudanar da zaben cikin lumana na nufin gwamnatin Somalia zata iya maida hankali wurin daukar matakan gaggawa a kan batutuwa kamar annobar COVID-19 da farin dango da kuma batun canjin yanayi da fari da suka shafi dubban dubatar mutane.

XS
SM
MD
LG