Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SSS Ta Kama Masu Zanga-zanga a Kaduna


Kakakin hukumar SSS, Marilyn Ogar.
Kakakin hukumar SSS, Marilyn Ogar.

Yunkurin hadakar kungiyoyin mata da matasan da suka zaman dirshen domin nuna damuwarsu game da tabarbarewar tsaro a Najeriya ya samu cikas, biyo bayan haramta taron da hukumar jami’an tsaro Farin Kaya a Jihar Kaduna tayi.

Yanzu hukumar SSS din ta fito da makamai, tana barazanar harbin fararen hula masu aniyar gudanar da zanga-zangar lumana.

Da yake nuna damuwarshi game da wannan mataki, shugaban hadakar kungiyoyin da suka shirya wannan zama da dirshen Komrade Ibrahim Garba Wala yace an riga an kama wasu mambobinsu mutum uku.

“Abun takaici shine, jami’an tsaro sun hana mu gudanar da wannan abu. Sun gayyace mu zuwa Ofis dinsu, wanda muka gani cewa tamkar dama ce wadda zamu yi aiki dasu, jami’an tsaro saboda samawa al-umma da mu da muka fito, samun tsaron da ya kamata,” inji Ibrahim Wala.

Mr. Wala ya cigaba da cewa “abun takaici shine, zaman da muka yi a Ofis din SSS, mun samu wajen sa’o’i biyu zuwa wajen uku tare da shi, shugabansu, sunce damu sam baza su yarda ba, saboda suna gani tamkar cewa wasu ne ke amfani damu saboda biyan bukatun kansu.”

“Wannan abun takaici ne, kuma abun rainin wayo ne, wadda muke cewa hukuma sun dade suna amfani da irin wannan yaudara, wadda shekaru 10 a baya, zasu ce maka ‘Kaduna akwai matsala kaza, saboda haka baza a iya irin wannan taro ba, saboda yana iya zama fitina na addini’,” inji Komrade Wala a fusace.

Komrade Wala ya cigaba da bada labarin abunda ya faru “bayan mun tashi daga ganawa, kawai mun kama hanya zamu tafi, wasu daga cikinmu suna kan hanyar fita, sai gashi ance wasu sunzo da bakaken kaya da bakar mota sun tsare mutum uku. Don haka, wannan kadai ya isa mu fito muyi zanga-zanga, bamu yarda ba! Wadanda ya kamata su tsare rayukan mutane, ko kuma su baiwa mutane damar ‘yancinsu suyi walwala, sune ake hada baki dasu.”

Sashen Hausa na Muryar Amurka yayi kokarin jin ta bakin jami'an SSS na Jihar Kaduna, amma ba'a samu nasara ba, saboda Isah Lawal Ikara ya kira mataimakin darektan hukumar, wanda aka yi wa bayanin halin da ake ciki, sai ya kashe waya, kuma an kira shi sau uku daga baya, amma bai amsa waya ba.

Shi kuwa kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Kaduna, SP Aminu Lawal cewa yayi bashi da masaniya gameda wannan batun.
XS
SM
MD
LG