Accessibility links

Su Kwankwaso ne Bata Garin APC - in ji Shekarau


Mallam Ibrahim Shekarau a lokacin da ya zama dan takarar jam'iyyar ANPP a birnin Abuja, 15 Jan 2011.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau ya koma jam’iyyar PDP mai mulki a Najeriya.

Mallam Shekarau wanda ya tabbatar wa Muryar Amurka haka ne a hira da yayi da manema labarai inda ya furta cewa kowace jam’iyya tana da mutanen kirki, da na banza.

Mallam Shekarau yace “Ni duk wanda zai yi mun adalci, ya sani tun shigowata siyasa, nakan banbance tsakanin sunan jam’iyya, da ‘ya’yan jam’iyya. Kullum ina gayawa mutane cewa babu jam’iyyar da babu na kirki, babu jam’iyyar da babu shakiyyi.”

“Kuma kullum ina gayawa mutane cewar mu akidar mu shine ranar kiyama, Allah ba sunnan jam’iyya Zai tambaye ka ba, wadanda kake muamalla da su a wannan jam’iyya. Don haka, zargi da muke wa PDP, mun san suna da mutane na gari, kukan mu shine akwai wasunsu wadanda suke kama karya, suna cutarwa, suna danne hakkin mutane”, a cewar Shekarau.

Gwamnan wanda yayi takarar shugaban kasa a shekarata 2011 ya bada misalai.

Yace “a nan Kano, ba karya bane, karkashin jagorancin mai girma gwamnan jihar Kano, a karkashin inuwar PDP, akayi zabe na cike gurbi a kananan hukumomin Gaya da Garko. Shi (Gwamnan) ne ya bada izini, da yawunsa da yaddarsa, aka debi ‘yan daba, aka debi lalatattu da makamai, suka fi karfin yawan wadanda zasu jefa kuri’a”.

“To yau aka wayi gari, irin wadannan mutane, irin wadannan masu wannan akida da kama karya, ta kwace ba demokradiyya ba, sune suka shigo APC, har ana rawar kafa cewa sun shigo, shine muka ce to mu, tunda sune bata garin PDP, yanzu sun shigo APC, sun zama bata garin APC, muka ce a ci lafiya.”

Dama tun bayan sauyin shekar jam’iyya da Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso yayi, daga PDP zuwa APC rigingimu suka taso dangane da shugabancin jam’iyyar a shiyyar jiha.

Da wakilin Muryar Amurka Mahmoud Ibrahim Kwari ya tambayi Mr. Shekarau ko hakan na da nasaba da wannan sabuwar shawara tasa, cewa yayi “na sha fada, ba rigima nake don wai ba’a ce sardauna ne leader ba, ko an ce gwamna ne leader, wannan walLahi ba shine a gabanmu ba.”

XS
SM
MD
LG