Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Kudu Na Jan Kafa Wurin Aiwatar Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya


Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir.
Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir.

Bangarorin da ke cikin yarjejeniyar zaman lafiyar Sudan ta Kudu sun kasa cimma wa’adi na yankin da aka basu ranar Lahadi da ta gabata da su rushe da kuma sake fasalin majalisa.

Sanarwar bayan taron ta ranar 14 ga watan Yuni wanda kungiyoyin kasashen Afirka ta Gabas (wato IGAD a takaice) wacce ke shiga tsakani a yarjejeniyar zaman lafiyar Sudan ta Kudu, ta yi kira ga shugaban kasa Salva Kiir da ya rusha majalisar dokoki kasar zuwa ranar 26 ga watan Yuli.

An kafa kwarya kawaryar gwamnatin hadaka kasar watannin biyar da suka gabata, amma har yanzu ba a sake fasalin majalisa ba kuma shugaban kasa Salva Kiir ya nada gwamnoni jihohi makonnin kadan da suka gabata.

Ministan yada labaran Sudan ta Kudu, Michael Makuei ya fada shirin South Sudan in Focus na VOA cewa bangarorin har yanzu suna kan gudanar da aiki na sake fasali majalisar dokokin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG