Sule Baban Nana ya ce kowa ya san irin ukubar da 'yan arewa maso gabashin kasar suka sha a hannun yan kungiyar Boko Haram. Ya ce an kashe matasan yankin an kuma karya tattalin arzikin nahiyar. Ya ce ta dalilin wuyar da aka sha bai kamata mutane kamar su Dr..Ahmed Datti da Malam Shehu Sani su juya ma kwamitin baya. Kamata ya yi su yi la'akari da hurucin Alhaji Shehu Lemu. A ganinsa tamkar son kai ne mutanen suka yi.
Ya gargadesu su yi wa Allah su sake tunanensu su taimaki arewa da kasar gaba daya.