Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Leko Ta Koma Ga Noor Salmar


Gidan da aka kama Noor Salman

A jihar Florida ta leko ta koma, ga matar mutumin nan da ya kashe mutane har 49 a wani gidan rawa. Domin kuwa alkali ya sake ta amma kuma wani alkali ya sake kama ta.

Noor Salmar ‘yar shekaru 31 da mijin ta mai suna Omar Marteen ya bude wuta a cikin taron jama’a a wani gidan rawa dake birnin Orlando, a ranar 12 ga watan yuni, da farko alkali ya sallameta amma kuma wani alkalin yace akwai bukatar tsananta bincike domin tantance ko tana da masaniya game da kashe mutane da mijinta yayi ko a’a.

Muddin dai aka same ta da laifi zata fuskanci zaman gidan yari har na tsawon rayuwurta.

To da farko dai, alkali Donna Ryu a ranar laraba ya yanke hukuncin cewa Salman bata da ko wane irin hadari, kuma bata da nasaba da kungiyar IS ko kuma ra’ayi irin nasu, Amma sai dai mai gabatar da kara yace tilas ne Salman taci gaba da zama a tsare domin ko daya daga cikin tuhumar da ake mata ya hada da aikin ta’adanci.

Sai dai Salman tace ita bata da laifi cikin wannan harin da mijin ta yakai a wannan gidan rawa, to amma Mai gabatar da kara yace abinda yake son ya sani shine idan tana da masaniyar cewar Mateen na shirin kai wannan harin ko kuma a’a.

Facebook Forum

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG