Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Ta Kaure Kan Inda Za A Bisne Mugabe


Shugaba Robert Mugabe
Shugaba Robert Mugabe

Yayin da al’ummar kasar Zimbabwe ke ci gaba da jimamin rasuwar tsohon Shugaban kasar Robert Mugabe, wanda ya rasu a karshen makon da ya gabata yana mai shekaru 95, hukumomin kasar sun ware ranar Asabar mai zuwa a matsayin ranar da za a yi jana’izar tsohon shugaban kasar.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da wasu rahotanni ke nuna cewa iyalan marigayin sun nemi da kada a binne shi a makabartar da aka ware domin gwarazan kasar ta Zimbabwe wacce ake kira da National Heroes Acre a Turance.

Rahotanni da dama sun ruwaito iyalan tsohon shugaban kasar ta Zimbabwe suna cewa, marigayin ya bar wasiyyar cewa kada a binne shi a makabartar kasar wacce aka tanada domin gwarazan kasar.

Sai dai wata sanarwa da hukumomin kasar suka fitar, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, ta nuna cewa a ranar Asabar za a yi jana’izar Mugabe, ko da yake, ba ta ambaci inda za a binne shi ba.

Rugare Gumbo, shi ne tsohon ministan Ma’aikatar kula da Tattalin Arzikin kasar ta Zimbabwe, a wata hira da ya yi da Muryar Amurka ta wayar Tarho ya ce bai ga abin kai ruwa rana a nan ba.

To ita dai gwamnatin kasar ta Zimbabwe ta musanta rade-radin da ake yi cewa an samu baraka tsakaninta da iyalan tsohon shugaban kan inda za a yi bison, amma ta ce, a nata tunanin, a wannan makabarta ya kamata a binne shi.

Tuni dai iyalan marigayi Mugabe da sarakunan gargajiyar yankin da ya fito, suka bayyana cewa sun yi nasu shirin dangane da jana’izar tsohon shugaban kasar, amma suna jiran amincewar gwamnati.

A ranar Jumma’ar da ta gabata tsohon shugaban ya rasu a Singapore bayan da ya yi fama da rashin lafiya. Marigayi Mugabe, ya kwashe shekaru 37 yana mulkin kasar ta Zimbabwe, kafin a kawar da gwamnatinsa a shekarar 2017.

A dai ranar Laraba ake sa ran za a mayar da gawarsa gida domin a yi mata jana’iza.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG