Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaitaccen Tarihi Da Wasu Halayen Marigayi J.J Rawlings Masu Jan Hankali


Marigari Jerry Rawlings
Marigari Jerry Rawlings

A cigaba da tabo wasu batutuwan tuna baya game da rayuwar marigayi tsohon Shugaban Ghana, JJ Rawlings, an dan tabo wasu halayyansa da su ka yi matukar banbanta shi da sauran shugabanni da kuma takaitaccen tarihinsa.

Yayin da duniya ke cigaba da nuna alhini game da rasuwar tsohon Shugaban Ghana JJ Rawlings, jiya Alhamis, tsohon jami’in tsare tsaren jam’iyyar NDC Baba Shariff, ya bada takaitaccen tarihin marigayin da kuma halinsa.

JJ Rawlings, wanda aka haife shi ranar 22 ga watan Yunin 1947, ya mutu ne a wani asibitin Accra babban birnin kasar Ghana ya na mai shekaru 73 a duniya.

Jerry Rawlings, AU envoy to Somalia, speaks to displaced people during a visit to camps in southern Mogadishu, July 20, 2011. (AP)
Jerry Rawlings, AU envoy to Somalia, speaks to displaced people during a visit to camps in southern Mogadishu, July 20, 2011. (AP)

Ya jagoranci juyin mulkin soji sau biyu a shekarar 1979 ciki har da kwace mulki da ya yi daga hannun soji ya mika ga farar hula kafin daga bisani ya jagoranci ‘yan siyasar kasar wajen kafa tsarin siyasa mai jam’iyyu da dama.

Marigayi Rawlings, wanda mahaifinsa wani baturen kasar Scotland ne, manomi kuma masanin kimiyyar harhada sinadarai da magunguna, mai suna James Ramsey John, Kuma mahaifiyarsa mutumiyar Ghana mai suna Victoria Agbotui, ya hallaka wasu tsoffin shugabannin kasar da janar janar na soji saboda jin hanci da rashawa. Hasali ma ya sa an bindige wani alkalin kotun kolin kasar a bainar jama’a bisa zargin rashin gaskiya.

FILE - Ghana's former President Jerry Rawlings arrives for the swearing-in of Ghana's new President Nana Akufo-Addo in Accra, Ghana, Jan. 7, 2017.
FILE - Ghana's former President Jerry Rawlings arrives for the swearing-in of Ghana's new President Nana Akufo-Addo in Accra, Ghana, Jan. 7, 2017.

Amma ana wa marigayin ganin mai matukar kishin kasa da kuma son adalci, gaskiya da rikon amana.

A wata hira da wakilin VOA Ridwan Abbas ya yi da Baba Shariff, ya ba da takaitaccen tarihin marigayin da kuma bayanin wasu halayyansa masu ban shawa'a:

please wait

No media source currently available

0:00 0:10:11 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG