Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takawa Nnamdi Kanu Birki Da Matasan Arewa Sukayi Ya Yi Daidai


 Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu

Matasan arewacin Najeriya sun gaji da rashin mutuncin Nnamdi Kanu shi ya jawo batun baiwa 'yan kabilar Igbo wa'adi.

An bukaci ‘yan Najeriya dasu kasance tsintsiyar madaurinki daya domin ci gaba da ka karuwar arzikin kasar.

Dr. Safiyanu Ali Maibiyar, wani mazaunin Amurka kuma mai sharhin akan alamuran yau da kullum ne ya bada shawarar a wata hira da muryar Amurka.

Yace kasance Najeriya dungulalliyar kasa shine alfanu ga daukacin kasar babu alfanu ga rabuwar kasar ganin irin halin tattalin arzikin da kasar ke fama da ita a yanzu.

Dr. Safiyanu, ya kara da cewa ya zama wajibi mahukunta su gargadi Nnamdi Kanu, akan irin kalaman da yake furtawa wanda ka iya jawo tashin hankali a kasar Najeriya, saboda haka ja masa kunne ya zama tilas.

Ya kara da cewa irin wadannan kalamai nashi shi ya jawo furushin da matasan arewacin Najeriya, suka yi na baiwa ‘yan kabilar Igbo, wa’adin cewa su kwashe su bar arewacin Najeriya. Wanda ya jawo ce ce ku ce a Najeriya da kasashen waje.

Amma ya kara da cewa matasan arewa suyi daidai da furucin da suka yi domin sun gaji da rashin mutunci Nnamdi Kanu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:08 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG