Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Taliban Sun Kaiwa Jami'an Tsaro Hari


‘Yan tawayen Taliban sun kai hari kan wani wurin zaman jami’an tsaro a yammacin Afghanistan, su ka kashe jami’an tsaron gwamnati akalla 11.

Harin na daren jiya Alhamis ya auku ne a gundumar Shindand da ke lardin Herat, mai iyaka da Iran.

Gwamnan Gundumar Shukrullah Shaker ya gaya ma Muryar Amurka cewa wannan harin na ‘yan tawaye ya kuma raunata jami’an tsaro hudu.

‘Yan sandan Afghanistan ne ke girke a wurin da ake kira Wurin-Tabbatar-da-Doka-da-Oda, a lokacin da aka kai masa harin, a cewar gwamnan. Shaker ya kuma tabbatar cewa babban jami’in tabbatar da doka na gundumar, wato babban jami’in ‘yansanda Sayed Sharafuddin Allawi, na daga cikin wadanda aka kashe din.

Wani mai magana da yawun kungiyar Taliban mai suna Zabiullah Mujahid, ya fada a wata takardar bayani da ta tura ma manema labarai cewa harin da aka kai a Shindand din, ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaron Afghanistan 20, kuma ‘yan tawayen sun yi awon gaba da motoci masu sulke da ake kira ‘Humvees’ wajen hudu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG