Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sallami Diyar Tsohon Jami'in Leken Asirin Rasha Daga Asibiti


Gwamnatin Burtaniya ta yi zargin cewa jami’an Rasha ne suka sanya masu wata guba dake illata jijiyar dan adam. Amma Rasha ta musanta zargin cewa tana da hannu a harin.

An sallami Yulia Skripal daga asibiti bayan da aka kai masu harin guba ita da mahaifinta a watan da ya gabata a Burtaniyya.

An tarar da Yulia da mahaifinta Sergei, wani tsohon jami’in leken asirin Rasha zaune akan benci a some, cikin mawuyancin hali kuma, ranar 4 ga watan Maris a birnin Salisbury da ke kudancin Burtaniyya.

Sun kasance a cikin mawuyacin hali na tsawon makonni har sai da suka fara samun sauki sosai.

Shugabar asibitin Gundumar Salisbury Christine Blandshard ba ta fadi lokacin da aka sallami Yulia ba, amma wasu majiyoyi sun ce jiya litinin aka sallame ta daga asibitin. A halin yanzu dai ba a san inda Yulia take da zama ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG