Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban Ta Yi Garkuwa Da Wasu Jami'an Aghanistan


Wani dan Taliban rike da bindiga

A kasar Afghanistan, 'yan kungiyar Taliban sun yi garkuwa da mutane da yawa bayan da suka dasa wani shingen bincike a kudu maso gabashin kasar.

Jami’ai a Afghanistan sun ce, ‘yan kungiyar Taliban sun yi garkuwa da wasu fasinjoji masu yawa a gabashin yankin da ke kusa da kan iyakar kasar Pakistan.

Bayanai na nuni da cewa lamarin ya faru ne a kusa da Gundumar Syed Karam, da ke kudu maso gabashin yankin Paktia.

Mazauna yankin sun ce, daruruwan ‘yan kungiyar ta Taliban sun gudanar da bincike akan motoci kusan talatin har na tsawon wasu sa’oi, kafin daga karshe su yi awun gaba da fasinjojin.

Babu dai wanda ya ya san inda mayakan na Taliban suka nufa da mutanen.

Kakakin kungiyar, Zabiuullah Mujahid, ya ce daga cikin wadanda suka yi garkuwar da su, akwai manyan jami’an gwamnatin Afghanistan guda takwas, ya kuma kore ikrarin da ake yi na cewa har da yara kanana a cikin mutanen.

Yanzu haka jami’an tsaron kasar sun kaddamar da wani shiri na kokarin ceto mutanen da aka kama.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG