Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tana Yiwuwa Iran Ta Halarci Taron da Manyan Kasashen Duniya Zasu Yi Akan Syria


John Kerry Sakataren Harkokin Wajen Amurka da zai jagoranci tawagar Amurka zuwa taron

Ma'aikatar harakokin wajen Amurka ta sanar cewa ana iya gayyato Iran zuwa wurin taron da zasu yi akan makomar Syria

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace ana sa ran za a gayyaci Iran wajen wasu muhimman taro game da makomar siyasar kasar Syria wanda za a yi wannan makon a Vienna.

A lokacin taron mai zuwa a ranakun Alhamis da Juma’a, Amurka da sauran kasashen duniya masu fada a ji, zasu tattauna akan abinda kakakin ma’aikatar John Kirby ya kira wani matakin siyasa mai sarkakiya.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ne zai jagoranci tawagar Amurka. Haka kuma halartar Iran zai zama wani matakin zakudawa gaba game tsakaninta da Amurka da kasashen duniya masu fada aji.

Musamman idan aka yi la’akari da yadda manyan kasashen duniyar ke kaucewa tsoma Iran a lamura in an dauke maganar yarjejeniyar da aka cimma ta Nukiliyar Iran a watan Yulin da ya gabata.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG