Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tanko Yakasai ya Kafa Wata Sabuwar Kungiya ta Dattijan Arewa


Tsohon ministan 'yan sanda na Najeriya, Dr. Ibrahim Yakubu Lame, da tsohon sakatren CPC, Buba Galadima, sun ce a kai kasuwa.

A yayin da Najeriya ta doshi gudanar da zabe a shekara mai zuwa, kungiyoyi sai kara kunno kai suke yi da sunan kare muradun al'umma ko makamantansu.

Tsohon dan siyasa Tanko Yakasai, ya jagoranci taron farko na wata sabuwar kungiyar da ya ba suna Majalisar Dattijan Arewa (Northern Elders Council), inda ya gayyato wakilai daga jam'iyyar PDP mai mulki, da kuma na jam'iyyar adawar nan da aka sani da sunan ACN domin tattauna abinda ya kira yunkurin da wasu keyi na tsoma hannun sarakuna a siyasa.

Tanko yakasai yace su na maraba da duk wani mai ra'ayi irin nasu da ya zo su hada kai domin cimma gurin wannan kungiya, ya kuma musanta cewa a shekararv 2011 ya kafa wata kungiya makamanciyar wannan wadda a karshe ta fito ta goyi bayan takarar shugaba Goodluck Jonathan.

Da yake mayarda martani kan ko me yasa shi kuma bai halarci wannan taron da aka ce an gayyaci kowa ba, tsohon sakataren jam'iyyar CPC na kasa baki daya, Injiniya Buba Galadima, ya kada baki yacei, "...ba na baranda, ba na sojan haya, balle a yi amfani da ni, don wani abin duniya, in cuci al'umma ta."

Tsohon ministan kula da ayyukan 'yan sanda, kuma sakataren kungiyar Tarayyar Arewa (Arewa Northern Union) wadda marigayi Dr. Olusola Saraki ya kafa, Dr. Ibrahim Yakubu Lame, ya ce yayi mamaki, kuma ya ji takaicin ganin cewa Tanko Yakasai, wanda yake dauka a zaman uba, zai yi irin wannan aikin wadda a fili na neman abin duniya ne.

Dr. Lame ya shawarci Yakasai da cewa a siyasance, wannan ba zamaninsu ba ne, don haka ya kamata ya gane cewa zamani ya canja. Yace ai Yakasai dan kungiyarsu ne, amma haka kwatsam ya fito yana ce ya kafa ta sa kungiyar.

Ga rahoton Nasiru Adamu el-Hikaya daga Abuja.

Tanko Yakasai ya Kafa Wata Sabuwar Kungiyar Dattijan Arewa - 2:51
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG