Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tanazania Na Kokarin Shawo Kan Wata Mummunar Zanga-zanga Yau Alhamis


sHUGABAN Tanzania John Magufuli

Zanga-zangar da aka shirya yau domin kin amincewa da yunkurin takaita harkokin siyasa da walwalar 'yan jarida ya tsoratar da gwamnatin kasar wadda yanzu tana neman shawo kan lamarin

Kasar Tanzania tana kokarin kawar da yiwuwar wata gagarumar zanga zanga a yau Alhamis, wacce aka shiryata ta kafafen sada zumunta domin nuna rashin amincewa takaita harkokin siyasa da walwalar yan jarida da hukuma tayi tun lokacin da shugaba John Magufuli ya hau mulki shekaru uku da suka shige.


Jami’ai a kasar da take gabashin Afrika kuma daya daga cikin kasashe mafi zaman lafiya a nahiyar, sun gargadi jama’a game da yin zanga zanga a kan titi. Haka kuma an shirya yin zanga zangar a ofisoshin jakadancin kasar dake kasashen waje ciki harda birnin Washington, inda wasu mutane da dama suka yi zanga zanga da safiyar jiya Laraba.


Wasunsu sun rufe huskokinsu, yayin da suka yi ta zagayaofishin jakadancin kasar ana yayyafi, kuma suna rike da kwalaye masu rubutu, tilas Magufuli ya tafi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG