Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarin Ma’aikatan Diflomasiyar Amurka Na Kan Hanyarsu Ta Dawowa Daga Rasha


Wasu manyan motocin safa-safa guda ukku aka hango yau Alhamis shake da mutane da kayansu suna barin harabar ofishin jakadancin Amurka dake birnin Moscow, sun tasarwa babban filin jirgin sama a daidai lokacinda wa’adin zaman kasar da Rasha ta yanke masu yake karewa.

Yanzu haka tarin ma’aikatan diflomasiyar Amurka na kan hanyarsu ta dawowa gida bayanda aka taso keyarsu daga Rasha a matsayin maida martini ga matakin da ita ma Amurka ta dauka kwanan baya a kan Rasha, na korar irin wadanan jami’an nata.

Duk wannan ya faru ne bayan harin gubar da aka kai a Ingila kwannakin baya akan wani tsohon jigon leken assiri na Rasha, abinda ake dora laifin kan ita gwamnatin ta Rasha.

An dai yi ta samun irin wannan zirga-zirgar ta jami’an diflomasiyar kasashe da dama da ake kora daga ma’aikatunsu na diflomasiya, tun bayan wannan farmakin na guba da aka kai akan Sergei Skripal da ‘yarsa, wanda Biritaniya ta ce an yi anfani da wata guba ce da aka san cewa sojan Rasha ne ke sarrafa ta.

Wannan al’amrin dai ya janyo lalacewar dangantakar Rasha da kasashen yammaci da dama, wanda a dalilinsa ne aka kori ma’aikatan diflomasiyar Rasha kamar 150 daga Amurka da kasashen dake cikin kungiyar Turai ta EU da wadanda ke a kungiyar tsaron Turai ta NATO.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG