Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Yaki Da Cin Zarafi a Najeriya


Farfesa Yemi Osinbajo a Taron Yaki Da Cin Zarafi a Najeriya

An kawo karshen taron yaki da cin zarafi na kasa da kasa da gidauniyar Aisha Buhari da hadin gwiwar gidauniyar tallafawa jama’a ta Majalisar Dinkin Duniya suka shirya a birnin Abuja

Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya nanata muhimmancin yin aiki tare da karfafa kudurori wajen kawo karshen cin zarafin mata da kananan yara da kuma kare hakkinsu a Najeriya.

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta ce dama can tana da niyyar gudanar da irin wannan taro amma bai samu ba sai wannan lokaci, inda ya zo ya hadu da abin da ya faru kwanakin baya wanda mata da miji suka yi fada har ta kai ga mijin ya rasa ransa.

Aisha Buhari Na Jawabi a Taron Yaki Da Cin Zarafi a Najeriya
Aisha Buhari Na Jawabi a Taron Yaki Da Cin Zarafi a Najeriya

A cewar Aisha Buhari, mutane da yawa sun yi ta jan hankalinta don daukar mataki, wanda hakan yasa ta shirya wannan taron mai taken “Yaki da Cin Zarafi” tare da hadin gwiwar gidauniyar tallafawa jama’a ta Majalisar Dinkin Duniya, wanda yanzu haka suke aiki a Najeriya kan cin zarafi.

Taron dai ya mayar da hankali ne domin tunkarar matsalolin cin zarafi da ya hada da cin zarafin kananan yara da safarar mutane mata da maza da kuma cin zarafin gajiyayyu ko tsofaffi sai kuma fada tsakanin ma’aurata da dai sauransu.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG