Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashe Tashen Hankula


Ta'adancin Boko Haram

Yawan tashe tashen hankulan da ake yi a Najeriya sai gwmnati ta yi da gaske kafin ta shwao kan lamarin

Tashe tashen hankali kamar ya zama ruwan dare gama gari a Najeriya. Babu wata mafita idan gwamnati bata tashi da gaske ba.

Wani masani ya ce abun da ban tsoro domin abubuwa na faruwa kamar babu hukuma a kasar. Sai gwamnati ta tashi ta fuskanci yakin da gaske ta kuduri aniyar gamashi. Ya kamata kuma ta bi duk hanyoyin da suka dace . In ma za'a yi sulhu a yi. Idan kuma yakin ne to sai a yi. Idan irin wannan ya cigaba duk wasu kungiyoyi dake da irin ra'ayinsu zasu shiga harakar. Ban da haka kungiya kamar Boko Haram tana da hanyar fadada ta'adancin da ta ke yi kamar kungiyar Al-Sahabab.Lokacin da ta fara a wani wuri karami ta soma amma yanzu ya yadu zuwa wurare da dama.

Akwai dokar tabaci a Maiduguri amma bata hana 'yan ta'adan yin abun da suke son yi ba. Abun mamaki ne a ce an samu 'yan bindiga sanye da rigunan soji kana su kone wurare su kuma hallaka jama'a da dama. Basu tsaya nan ba har da tare hanyoyi domin ta'adanci ba tare da sojoji sun biyo hayoyin ba. Saboda haka dole ne gwamnatin Najeriya ta yi takatsantsan. Idan ba gwamnati ta tashi tsaye ba lamarin sai cigaba da yin muni.

Da aka kwatanta abun da ya faru a Kenya da Najeriya ya ce menene gwamnati zata yi ya ce kungiyoyi irin na Kenya da Najeriya kungiyoyi ne da ka iya sayen makamai ta kowace hanya sannan kuma basu da riguna da z'a sansu. Suna iya rikidewa da mutane su yi barna. Don haka dole gwamnati ta dauki tsauraran matakai.

Ga karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG