Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Tagwayen Boma-Bomai A Jos

Tashin Bom (file photo)
Tashin Bom (file photo)

Wasu tagwayen boma bomai suntashi a kasuwar Taminus dake tsakiyar birnin Jos, inda aka sami rashin rayuka da yanzu haka hukumomi basu tabbatar da adadinsu ba.

Lamarin ya aukune da missalin karfe shida da rabi na yammaci yau Alhamis, a wajen shagon cin abinci na Mr Bigs, dake kusa da sha tale-talen Taminus, inda ake hada-hadar saida kayayyakin gwanjo, wakiliyar mu Zainab Babaji, ta zanta da wasu dake gurin da boma-boman biyu suka tashi.

Inda ta zanta da Ibrahim Abbas wanda yace, “ yanzun nan gashi muna gurin ne, kuma naga gawarwaki sama da guda bakwai yanzunnan, a yanzu hakama mota ta shiga gangarar ‘yan kwalli domin dauko wasu gawarwakin.”

Yakuma ce akwai ‘yan sanda da sojoji harma da ‘yan bigilanti a gurin wannan tashin hankali ya auku.

Har yanzu dai bamuji tabakin hukumomi ko jami’an tsaroba.

Idan ba’a manta ba a watannin baya ma wasu tagwayen boma bomai sun tashi a kasuwar ta Taminus, inda aka samu asarar rayuka da dama.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG