Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Da China Ke Yi Kan Kafafen Yada Labarai A Duniya Na Karuwa-Freedom House


ADAMAWA: Masu sayar da jaridu
ADAMAWA: Masu sayar da jaridu

Najeriya ce kasar da ta fi fuskantar barazanar da China ke yi na kokarin yin tasiri akan kafafen yada labarai a duniya, in ji wani rahoton da Freedom House ta fitar a ranar Alhamis.

A lokacin da Dapo Olorunyomi, mawallafin jaridar Premium Times ta Najeriya, yana makaranta a shekarun 1970, ya tuna a cikin wasikun da yake samu "mujallun kasar China masu sheki wadanda aka aiko da su a kyauta, suna bayyanarwa da kuma yaba wa irin ci gaban da kasar China ta samu."

Dabarun yada labaran China a Najeriya na kara yin tasiri sosai tun a lokacin, in ji Olorunyomi

Najeriya ce kasar da ta fi fuskantar barazanar da China ke yi na kokarin yin tasiri akan kafafen yada labarai a duniya, in ji wani rahoton da Freedom House ta fitar a ranar Alhamis.

Freedom House kungiya ce mai zaman kanta ta Washington wadda ke mai da hankali kan 'yancin dan Adam da dimokaradiyya.

A duk fadin duniya, China ta kara kaimi a gangaminta na yin tasiri kan kafofin watsa labaru na duniya, yayin da kokarin nata ya karu tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021 a cikin kasashe masu dimokaradiyya 18 daga cikin 30 da Freedom House ta gudanar da bincike a ciki.

Baicin yukunrin China na yin tasiri a kafafen labaran kasashe masu dimokaradiyya, rahoton ya kuma duba martanin da kasashen suka bayar, wanda daga nan aka kirga su kan jajircewa.

An ga wata mujalla mai dauke da shugaban kasar China Xi Jinping mai taken "Kasar China ta kara karfi" a wani dandalin labarai a birnin Beijing na kasar China, a ranar 21 ga Oktoba, 2017.

Jam'iyyar Kwaminisanci ta kasar China (CCP) tana amfani da dabaru iri-iri, kamar yadda Freedom House ta gano, ciki har da yawan rarraba abubuwan da gwamnati ta shirya, da cin zarafi da kuma tsoratar da ma’aikatun cikin gida, da auna labaran karya, da kuma yin amfani da cin zarafin yanar gizo da shafukan sada zumunta na bogi.

Babbar manufarta, a cewar Freedom House, ita ce ta rinjayi ra'ayin jama'a don samun tagomashi, wani lokacin a matsayin hanyar tabbatar da saka hannun jari a kasashen da ake aunawa.

"Gwamnatin kasar Sin tana yin amfani da dabaru na zamani, da boye-boye da kuma tilastawa, kamar cin zarafi ta yanar gizo, ko kai hari ta yanar gizo, ko kuma kiran waya kawai ga 'yan jarida, don kokarin matsa lamba da yin tasiri wajen daukar labarai a kasashen duniya," in ji Sarah Cook, darektar bincike a Freedom House a kan China, Hong Kong da Taiwan, kuma daya daga cikin wadanda suka rubuta rahoton.

Ofishin jakadancin China da ke Washington ya nuna wa Muryar Amurka sharhin baya-bayan nan da ma'aikatar harkokin wajen China ta yi. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Mao Ning ya yi watsi da rahoton na Freedom House da cewa karya ce kuma "an gudanar da binciken kan manufar son zuciya."

Mao Ning ya ba da labarin jam'iyyar kwaminisanci ta kasar China (CPC) da gabatar da sahihin ra'ayi mai ma'ana daban-daban da ra'ayi game da kasar China ga duniya, wani bangare ne na aikin kafofin yada labaru da harkokin waje na kasar China. "Za mu ci gaba da bai wa duniya labarin kasar China."

Martanin ya bambanta daga kasa zuwa kasa, in ji Angeli Datt, mai nazari a kan China gidan Freedom House, kuma daya daga cikin wadanda suka rubuta rahoton.

Datt ya rubuta a cikin imel ga Muryar Amurka cewa, "A wasu kasashe lamarin yana da sauki kamar dai buga labarai masu mahimmanci amma kuma a wasu kasashen, kamar Taiwan, kungiyoyin farar hula ne ke shirya zanga-zangar dubban jama'a don nuna adawa da katsalandan jami’iayar kwaminisanci ta CCP a cikin tsarin labarai." "Girmar yanki da harshe iri-iri ya nuna cewa jajircewa a kan tasirin CCP ya bazu a fadin duniya gaske."

XS
SM
MD
LG