Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Farashin Dala Kan Kasuwanci a Najeriya


Takardar kudin Naira ta Najeriya

A yayin da farashin Dala ke ci gaba da tashi a kasuwanin bayan fage na Najeriya sakamakon matakin daina ba ‘yan canji kudi da babban bankin kasar ya dauka, darajar Naira na ci gaba da faduwa.

Samun kudin Dala ga masu tafiya don gudanar da kasuwanci, neman lafiya ko ilimi daga bankunan Najeriya abu ne mai cike da sharudodi da suka hada da ba da wasu takardun shedar bukatar hakan, wanda a wasu lokutan dole masu bukatar gaggawa su je su nema a kasuwar ‘yan canji.

Masana harkar tattalin arziki irin su Kasim Kurfi, na danganta tashin farashin kayayyaki a kasuwanin kasar da faduwar kudin Naira sakamakon yadda ake shigowa da yawancin kayayyaki daga kasashen waje.

Bayan haka ‘yan Najeriya da yawa ba sa ajiye kudinsu a Naira sai Dala a cewarsa.

Shi ma masanin tattalin arzikin kasa Dakta Isa Abdullahi, ya alakanta tashin Dalar da yadda ‘yan Najeriya ke nuna bajintar sayan kayan waje akan na cikin gida.

A cewar Abdullahi, tsarin yanayin tattalin arzikin Najeriya ya ta’allaka ne kan kasashen waje, kuma duk kasar da ba za ta iya samar da abubuwan da ake bukata a cikin gida ba to lallai za a fuskanci matsala.

‘Yan kasuwa, musamman masu kawo kaya daga kasashen waje na ci gaba da kokawa game da tashin farashin Dala, lamarin da ke tasiri sosai ga kasuwancinsu na yau da kullum.

A baya dai babban bankin Najeriya ya ce zai hukunta duk wanda aka samu da laifin amfani da takardun bogi wajen samun kudin dala, bayan samun labarin wasu mutane da ke amfani da wannan damar don samun riba.

A halin yanzu, farashin Dala a kasuwanin bayan fage ya kai Naira 570 a kan ko wacce Dala, abin da ya haifar da gibi akan yadda bankuna ke badawa kan Naira 415.

Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00


An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG