Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Ni Yin Tattaki Daga Legas Zuwa Abuja - Malam Isa


Shugaba Muhammad Buhari dake neman sake tsayawa zabe

Malam Isa Muhammad Munlaila wanda yace yana adawa da sake tsayawar Shugaba Muhammad Buhari takara ya fara tattaki daga Lagos zuwa Abuja jiya Alhamis kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Jaridar Vanguard ta yanar gizo ta jiya Alhamis ta rubuta rahoton cewa wani mutum mai suna Malam Isa Muhammad Munlaila dan asalin jihar Borno dake adawa da sake tsayawar Shugaba Muhammad Buhari takara ya soma tafiya a kasa daga Lagos zuwa Abuja.

Isa Muhammad Munlaila ya dauki matakin ne a madadin matasan Nigeria da ya ce an yi masu alkawarin ayyuka da zara Buhari ya zama shugaban kasa. Saboda haka suka hada kai suka zabi shugaban, amma kaico, ya ba su kunya. Maimakon kirkiro ayyuka miliyan uku kamar yadda ya yi alkawari cikin shekaru uku abun da aka samu basu wuce 500,000 ba.

Malam Isa Muhammad Munlaila ya ce babu wanda ya zuga shi ko tunzura shi ya dauki matakin da ya dauka. Ya ce yana yi ne ba domin kudi ba, yana da nashi kudin. Kazalika ba ya cikin wata jam’iyyar siyasa. Yana wakiltar matasan Nigeria ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG