Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TEXAS: Wani Asibiti a Jihar Bashi da Kwarewar Kula da Mai Cutar Ebola


Ma'aikatan kiwon lafiya - Cutar Ebola

Rahoton da wata kungiyar kwararru mai zaman kanta ya nuna cewa wata asibiti a jihar Texas bata da horon kula da wadanda suka kamu da cutar ebola

dake kudancin Amurka bata cikin shirin kulawa da mutum na farko da aka taba samu dauke da cutar Ebola anan Amurka ba, haka kuma bata san yadda zata kare maaikatan asibitin da suka kula da masu aikin ungwazomanci guda biyu da suka kamu da cutar ba.

Rahoton wanda aka bayar a yau Jumaa ya bayyana bisa ga dukkan alamu, maaikatan cikbiyar yaki da cututtuka ta Amurka da sauran cibiyooyin kiwon lafiya na Amurka suna tafe suna koyon hanyoyin sarrafa wannan al’amarin ne tare sauran maaikatan wannan asibitin ta Presbyterian dake birnin Dallas.

Mutumin da ya kamu da cutar ebola,Thomas Eric Duncan dan kasar Liberia mazauni nan Amurka shine na farkon daya tafi asibitin na Dallas ran 25 ga watan satunbar shekarar data gabata da niyyar neman taimakon gaggawa sakamakon ciwon kai, mura, sai jikin sa da yayi zafi sosai amma ya rasu daga bisani.

Sai dai abinda ba a gane ba shine dalilin da yasa wanda ya kamu da zazzabi lokutta da dama ba a sake binciken sa kafin a sallame shi daga asibiti, ko ma idan su likitocin dake kula dashi sun fahinci cewa zazzabin nasa ya karu

Binciken ya bayyana cewa bayanan da wata maaikaciyar asibitin ta karba dangane dashi Duncan yayi zuwa Africa ba’a bayyana shi ga likitoci ba illa dai kawai ta shigar da bayanan a cikin naurar tattara bayanai na kiwon lafiya na asibitin.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG