Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

THAILAND: An Kama Wasu Jami'an Soji Da 'Yan Sanda Da Laifin Safarar Mutane


Wani janar a kasar Thailand yana cikin mutanen da aka samu da laifin safarar bil’adama a kasar.

Yau laraba alkali ya fara yanke hukumci a kan sama da mutane dari da ake tuhuma.

An kama mutanen da ake tuhuma da suka hada da jami’an soji, da ‘yan sanda da kuma ‘yan siyasa ne a shekarar dubu biyu da goma sha biyar bayanda aka gano gawarwakin mutane da dama a wadansu kaburkura marasa zurfi cikin sunkuru, kusa da kan iyakar Thailand da Malaysia.

Kaburkuran suna kusa da wani sansani da masu safarar mutane suke tsare ‘yan ci rani sai iyalansu sun biya kudin fansa. Da dama suna mutuwa sabili da rashin abinci, da kuma zazzabin cizon sauro.

‘yan ci ranin sun hada da ‘yan kabilar Rohingya Musulmi dake gujewa tashin hankalin da ake yi a jihar Rakhine ta Myanmar, da kuma ‘yan asalin kasar Bangladash dake tafiya neman aiki a Thailand da Malaysia da kuma Indonesiya.
Daga cikin wadanda aka samu da laifi, akwai laftanar janar Manas Kongpaen, jami’in soji mafi girma da aka tuhuma.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG