Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Zata Gina Katanga A Iyakarta Da Afghanistan


Iyakar Afghanistan da Pakistan
Iyakar Afghanistan da Pakistan

Pakistan ta ce zata yi gaban kanta dagane da batun tsaro a yankin da kuma sa ido akan 'yan Afghanistan

Kasar Pakistan ta ce ta fa lura cewa tilas ne ta gina katanga a iyakarta da Afghanistan, saboda rashin hadin kai daga bangaren hukumomi a Kabul.

Yankin kan iyakan ya dade ya na zama wani sanadin rashin jituwa, ta yadda kungiyoyin mayaka, da 'yan ta'adda da 'yan fasakwabri ke amfani da wannan yanki mai cike da tsaunuka.

Pakistan ta ce yanzu za ta yi gaban kanta wajen tabbatar da tsaro a yankin, za kuma ta rika sa ido kan miliyoyin 'yan Afghanistan da ke gudun hijira a Pakistan.

Kasar Afghanistan dai na adawa da gina katanga a kan iyakar, kuma ba ta amince da inda aka shata kan iyakar ba, wadda hukumomin tsohuwar gwamnatin mulkin mallaka ta Burtaniya na yankin Indiya na da su ka shata.

Shugabannin Afghanistan na kuma zargin sojojin Pakistan da kuma hukumar leken asirin rundunar sojin Pakistan da taimakawa wa mayakan Taliban da kuma kungiyar Hakkani mai alaka da Taliban din don su cigaba da yake-yaken sari ka noke a Afghanistan.

Wadannan zarge-zargen sun dade su na kawo rashin jituwa, sai kuma ga wannan shirin gina katanga da Pakistan ke yi, wanda ya dada rigita abubuwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG