Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Na Halartar Taron MDD a Karon Farko


Shugaba Trump yana wata liyafa da shugabannin kasashen yankin Latin Amurka a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya
Shugaba Trump yana wata liyafa da shugabannin kasashen yankin Latin Amurka a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban Amurka ya kwashe yinin ranar Litinin yana ganawa da shugabannin daban daban yayin da yake halartar taron Majalisar Dinkin Duniya a karon farko inda zai yi jawabinsa a yau Talata.

Shugaban Amurka Donald Trump ya wuni yana ta halartan dumbin tarukka inda ya gana da manyan mutane masu yawa, lokacin da ya fara hidimomin kwannaki hudu dake da alaka da babban taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya da aka soma a birnin New York.

Wannan shi ne karon farko da shugaban na Amurka zai fara halartar taron tun bayan da ya dare kan karagar shugabancin Amurka.

Idan dai ba a manta ba lokacin da Trump din yake yakin neman zabe ya sha sukar majalisar inda yakan bayyana ta a matsayin kungiya mara karrama dimokuradiyya ko kuma 'yancin dan adam.

Amma kuma sai ga shi yanzu da ya zama shugaban kasa yana yaba majilisar da cewa ba shakka tana da abubuwan da za a amfana a gare ta, tare da jinjina wa kwamitin sulhun na Majilisar na jefa kuri’ar data yi na saka wa Korea ta Arewa tsattsauran matakai game da gwajin da ta yi na makamin nukiliya.

Yau ne dai ake sa ran shugaban zai yi jawabinsa na farko a zauren majalisar a matsayin na shugaban Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG