A jawabinsa na farko ga Amurkawa da aka watsa kai tsaye daga ofishinsa na Oval office, a daren jiya Talata, Trump ya bayyana bukatarsa ta gina bango akan iyakar Amurka da Mexico, amma bai ayyana dokar ta baci ba, wadda za ta bashi damar gina bangon ba tare da amincewar Majalisa ba.
Shugaba Trump ya ce “A yau ina magana da ku ne saboda akwai karuwar matsalolin jin ‘kai da na tsaro, a iyakar kudancin kasarmu. A kullum jami’an shige da fice da dogarawan bakin iyaka, suna fuskantar dubban bakin hauren dake kokarin shiga kasarmu ta barauniyar hanya. Yanzu haka bamu da sauren wajen da zamu ajiye su, kuma bamu da wata hanya da zamu mayar da su kasashensu.”
Ya ce ya yin da Amurkawa ke cutuwa daga abin da ya kira matsalar bakin hauren da aka kasa shawo kanta, Trump ya ce bakaken fatar Amurka da hispaniyawa ne abin ya fi shafa sosai, saboda ayyukan yi da suke rasawa dalilin bakin hauren dake shiga kasar ba tare da izini ba.
Trump ya ce ‘yan Jam’iyyar Democrats sun ki amincewa da matsalar dake addabar kasar akan iyaka, kuma ya sake zargin su kan rufe wasu ma’aikatun gwamnatin kasar, wanda dagewar da suka yi na kin biyan kudin gina Katanga ta janyo.
Da take mayar da martani a madadin ‘yan jam’iyyar Democrats, kakakin Majalisar Wakilai Nancy Pelosi, ta zargi shugaban da zabar saka tsoro a zukatan al’umma, maimakon hada kai domin samar da masalaha.
Ga fashin bakin Kabiru Isa Jikamshi dan jarida a Washington a kan jawabin Trump:
Facebook Forum