Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Hada Beata 'Yar Guatemala Da Dan Ta Darwin


Shugaba Donald Trump

Hukumomi a Amurka sun hada wata ‘yar kasar Guatemala da dan ta mai shekaru bakwai a yau Juma’a bayan an raba su watanni da dama a kan iyakar Amurka.

An hada Beata Mariana de Jesus Mejia-Mejia da dan ta Darwin ne a filin saukar jiragen sama na Baltimore da Washington a jihar Maryland. Wuni guda kafin su hadu, ma’aikatar shari’a ta amince a saki Darwin ya koma wurin mahaifiyarsa da take gaban shari’a.

Wannan mace ta bukaci mafakar siyasa tare da dan ta ne a lokacin suka tsallaka iyaka. Su biyun suna kan hanyarsu ne zuwa Texas, inda zasu zauna kafin a tabbatar da basu mafakar siyasar.

Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci hukumomin kasar a jiya Alhamis da su hada iyalan bakin hauren da suka tsallako daga kasar Mexico ta barauniyar hanya.

Trump ya fada a wata ganawa da ya yi da manyan jami’an gwamnatinsa a jiya Alhamis, yayin da uwargidansa Melania Trump take ziyara a inda ake tsare bakin hauren, yana mai cewar zamu hada iyalan wuri daya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG