Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Janye Dakatar Da Taimakon Kasashen Waje Da Amurka Ke Yi


Bayan da ya fuskanci matsin lamba daga bangarorin yan majalisa daga Republican da Democrats ya janye shawarar da ya yanke ta dakatar da taimakon da Amurka ke ba wa kasashen waje.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya dau shawarar yanke taimako da Amurka ke baiwa kasashen waje cewa barna ce kuma bai dace ba, amma kuma ya janye bayan da wasu manyan ‘yan majalisa suka kalubalanci shawararsa.

Shugaban kasar ya fito karara ya fada cewa akwai barna da almubazzaranci a taimakon da Amurka ke ba wa kasashen waje, ya kuma ce yakamata a sa hankali akan inda kudaden Amurka ke shiga, inji wani babban jami’in fadar Wahite House ya fadawa Muryar Amurka, ya ce dalili kenan da shugaban ya bukaci gwamnatinsa ta duba wannan lamari.

Sai dai ‘yan majalisar dokoki na bangarorin Republic da Democrats sun bayyana damuwarsu ga matakin da fadar White House ta dauka na dakatar da taimakon kasashen waje da majalisun tarayya suka rattaba hannu akai.

Wani hadimi a fadar White House yace akwai mutane da dama a majalisa da basu ra’ayin a yanke kudaden da ake barnatarwa wurin taimakawa kasashen waje.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG