Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Nemi Comey Ya Dakatar Da Bincike Kan Flynn


Ratonni da aka wallafa sunce shugaban Amurka Donald Trump ya nemi tsohon shugaban hukumar binciken aikata laifuffuka ta FBI, James Comey, da ya dakatar da binciken da yake gudanarwa kan mai baiwa Trump ‘din shawara kan harkokin tsaron cikin gida Michael Flynn akan dangantakarshi da ‘kasar Rasha, amma fadar white House ta musanta rahotanin.

Rahotannin sunce Trump ya nemi wannan alfarmar ne gurin Comey lokacin wata ganawa da suka yi a watan Fabarairu. Kamar yadda wata takarda da Comey ya rubuta bayan ganawar ta su, shugaba Trump ya ce “Ina fatan dai zaka bar wannan ya wuce,” yana magana ne kan binciken da ake yiwa Flynn. Jaridar New York Times da ake bugawa a birnin New, ce ta fara bada wannan rahoto gameda bayanan wannan takarda da Comey ya rubuta, da ga bisani kuma jaridar Washington Post da ake bugawa anan birnin Washington DC da wasu kafofin yada labarai suka tabbatar.

Amma kuma, wata sanarwa da fadar White House ta ce rahotan babu gaskiya cikinsa, kuma ba haka tattaunawar ta kasance tsakanin shugaban ‘kasa da Mista Comey ba. ta kuma ‘kara da cewa shugaban ‘kasa ya sha nanata ra’ayinsa kan cewa Flynn mutumin kirki ne, kuma bai taba neman Comey ko wani mutum ba da ya dakatar da kowanne irin bincike da ya hada da tsohon mai bashi shawara kan harkokin tsaron cikin gida ba.

Haka kwatsam ba zato shugaban Trump ya sallami Comey a makon da ya gabata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG