Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Sake Nuna Alamun Zai Tattauna Da Kim Jong Un


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

A wani sakon Twitter da ya aike a daren jiya Juma'a, shugaban Amurka ya ce, akwai alamu da ke nuna cewa za a maido da shirin tattaunawar da zai yi da takwaran aikinsa na Korea ta Arewa Kim Jong Un bayan da ya soke ta a baya.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana kyakkyawar fata kan tattaunawar da za su yi da takwaran aikinsa na Korea ta Arewa, a ranar 12 ga watan Yuni mai zuwa, yana mai cewa ana samun ci gaba a tattaunawar da bangarorin biyu suke yi wajen maido da ganawar.

A wani sakon Twitter da ya aike a daren jiya Juma’a, Trump ya ce akwai yiwuwar zai kasance a Singapore a wannan rana da aka tsayar, kuma ba mamaki ma, za a iya fadada tattaunawar har ta wuce wannan ranar.

Sabuwar matsayar da shugaba Trump ya dauka, na zuwa ne bayan da hukumomin Korea ta Arewa suka nuna sha’awarsu ta a tattauna, duk da cewa ya soke zaman kamar yadda aka tsara.

Amurka ta soke ganawar ce a ranar Alhamis, bayan abin da ta kira barazana da Korea ta arewan ke yi na ficewa daga tattaunawar, lamarin da ya sa masu sharhi ke ta tsokaci a kai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG