Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Yabawa Masu Zanga-zangar Kin JInin Gwamnatin Iran


Shugaba Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya yabawa masu zanga-zangar Iran, yana mai cewa daga karshe sun ‘dauki mataki akan gwamnatin Tehran maras adalci da gaskiya, duk da cewa shugaban Iran ya zargi abokan gabar gwamnatin kasar da laifin tayar da mummunar zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Trump ya kafe a kafar Twitter cewa dukkan kudaden da tsohuwar gwamnatin shugaba Barack Obama, ta baiwa Iran “a cikin wauta”a matsayin wani bangare na yarjejeniyar kasa da kasa ta shekarar 2015 wadda ta kayyade shirin nukiliyar Iran, kudaden sun tafi harkar ta’addanci da kuma aljihun wasu mutanen ne kawai.” Trump yace, mutanen kasar ta Iran basu da isasshen abinci, ga matsalar tashin farashi da kuma rashin ‘yancin dan adam.

Jakadiyar Amurka a MDD, Nikki Haley, ta ce Amurka zata nemi a kira taron gaggawa na kwamitin sulhun MDD, domin tattauna zanga-zangar Iran, wadda ta lakume akalla rayuka 21 a cikin kwanaki shida.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG