Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Yace Amurka Da China Zasu Yi Kasuwanci


Shugaban Amurka Trump da na China Xi
Shugaban Amurka Trump da na China Xi

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi hasashe a jiya Talata cewa, Amurka da China zasu samu kyakkyawar alakar cinikayya, kuma yace alakar kasuwanci tsakaninsu zata bambanta a kan abin da aka saba gani karkashin shugabannin da suka shude.

Da yake jawabi da shugabannin 'yan kasuwa da ya gayyacesu, Trump yace yana son China ta cimma bukatunta, amma kuma yana so manufofin kasuwancinta su yiwa Amurka adalci.

Trump ya sha auna China a kan abin da yake cewa bata adalci a alakar kasuwancinta, kana yace yana so ya gayara al’amura ta yanda Amurkawa ma’aikata zasu amfana da wannan alakar. Trump ya aiwatar da wani shirin dora haraji na dala biliyon 30 a kan kayayyakin China, kana kuma ya fada a jiya Talata cewa akwai wani sabon shirin karin harajin dala biliyon 16 da zai fara aiki zuwa karshen wannan wata.

China ta fada cewa ta shirya ta mai da martanin harajin biliyoyin dala a kan kayayyakin Amurka dake shiga kasarta. Ta kuma fitar da wata sanarwar a kan sababbin alkalumma na karuwar fitar da kaya zuwa kasashen waje a cikin watan Yuli, duk da matakan da Amurka ke dauka a kanta.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG