Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Yana Shirya Sabon Tsari Akan Bakin Haure


Donald Trump, shugaban Amurka mai jiran gado

Bisa ga firar da yayi da gidan talibijan din NBC da alamu sabon shugaban kasar Amurka mai jiran gado yayi sassauci akan makomar bakin haure

Shugaban kasar Amurka mai jiran gado ya amince a jiya Laraba cewar zai zama shugaban kasa a daidai lokacin da siyasa ta rarraba kan al’umman kasar, sai dai ya musunta cewa yana da hannu a rarrabuwan kawuanan.

Trump ya fadawa gidan telibijin NBC cewa bai raba kan jama’a ba.

A wannan hira da ya yi da NBC Trump ya tabo abubuwa da dama.

Kodayake ya bada muhimmanci a kan batun bakin haure a lokacin yakin neman zabe da zancen gina bango tsakanin Amurka da Mexico har ma yace zai mai da baki zuwa kasashensu, Trump yace a halin yanzu yana tsara wani shiri wa mutanen da aka shigo dasu Amurka a matsayin yaya amma ba bisa doka ba.

XS
SM
MD
LG