Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Zai Sake Sa Hannu Kan Wata Dokar Hana Baki Shiga Amurka


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

A yau Litinin ake sa ran shugaban na Amurka zai sanya hannu kan sabuwar doka da zata haramtawa wasu rukunin mutane shigowa Amurka, wannan matakin ya biyo bayan da wata kotun daukaka kara ta dakatar da aiki da mfani da dokar ta farko.

Rahotanni a kafofin yada labaran Amurka suka ce, a karkashin wannan sabuwar dokar, kasar Iraqi bata jerin kasashe da galibin al'umarsu musulmi ne da dokar ta wucin gadi kan shige da fice ta shafa ba.


A dokar ta farko da Mr. Trump ya sanyawa hanu ranar 27 ga watan Janairu, kasashen Iraqi da Iran, da Libya, da Somalia, da Sudan da Syria da Yemen ne dokar ta shafa.


A halin da ake ciki kuma, jami'an shige da fice na Amurka sun tsare wani magidanci da iayalansa su biyar da suka sauka a tshar jirgin sama dake Los Angeles, kan hanyarsu ta zuwa birnin Seattle inda zasu zauna.
Wata takardar kara da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasa da kasa ta shigar gaban wata kotu a madadin mutumin da matarsa, da yara, ta bukaci kotun ta bada umarnin a sake su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG